Taron Sidney a game da cutar Sida | Labarai | DW | 23.07.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron Sidney a game da cutar Sida

A birnin Sydney na ƙasar Australiya,ƙurrarun massana ta fannin kiwan lahia fiye da dubu 5, daga ƙasashe 130 na dunia, na ci gabada tabka mahaurori,a game da cutar Sida.

A ranar farko ta wannan gagaramin taro, massanan sun yi imanin cewar,matakinyin kungullum ko kuma kaciya ga mazaje na taimakawa matuƙa gayya, wajen rage yaɗuwar cutar Sida.

Wani hasashe da su gabatar ya gano cewar, a yankin Afrika kudancin Sahara, inda cutar ta fi ta´adaci, daukar matakin kungullum ko kaciya, zai dalilin raguwa da kimanin milion 6, yawan mutanen da za su kamuwa da cutar , ya kuma ceci rayukan mutane a ƙalla milion 3, nan da shekaru 20 masu zuwa.

A game da haka mahalarta taron Sydney sun yi kira ga shugaban Afrika, su bada himma wajen waye kann jama´a a game da matakin yin sallatazuwa, ko kaciyya.

Sannan sun buƙaci ƙasashe ,masu hannu da shuni, su himmantu wajen ƙara yawan kudade, na gudanar da binciken hanyoyin taka birki ga cutar Sida.

Rahoton Majalisar Ɗinkin Dunia, ya nunar da cewar ayanzu haka, akwai mutane fiye da milion 40, wanda ke ɗauke da ƙwayoyin cutar Sida a dunia.