Taron shuwagabanin kasashe 7 na yanki kudancin Asia | Labarai | DW | 14.11.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron shuwagabanin kasashe 7 na yanki kudancin Asia

A birnin Dakka na India, shuwagabanin kasashe 7 na kungiyar hadin kai da tuntubar juna ta yankin kudancin ASia sun kammala zaman taron yini 2.

Kungiyar ta kunshi kasashen Bangladesh, Butan, India, Maldiva, Nepal, Pakistan da Sri Lanka.

Sanarwar karshe taron ta bayyana kuddurin wannan kasashe na gama karfi da karfe, ya junan su, domin yaki da talauci a tsawon shekaeru 10 masu zuwa.

Kasashen baki daya, na da jimmilar mutane billiar daya da million dubu dari hudu, wanda mafi yawan su ke fama da talauci.

Mahalarta taron sun amince su karbi kasar Afganistan a matsayin memba cikin wannan kungiya.

Kazalika sun cimma daidaito a kan batun girka hukuma ta musssaman domin riga kafi ga billa´o´i irin su Tsunami da girgiza kasa.