1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron shugabannin kudancin Afrika a Tanzania

March 29, 2007
https://p.dw.com/p/BuOp

Kakakin shugaba Robbert Mugabe yayi kira ga shugabannin kasashen nahiyar Afrika dake kammala taron yini biyu a birnin Darussalam din kasar Tanzania ayau ,da kada su dauki matakai na ladabtarwa akan sa, saboda matsalolin da kasar ta tsinci kanta ciki,inda ya danganta matsalar da kasashen yammaci na turai.George Charamba ya fadawa shugabannin Afrikan cewa cire mugabe ba shine bakin zaren warware rikicin ba,amma kira ga premier Tony Blair da mukarrabansa su cire takunkumin da suka dorawa kasar ta Zimbabwe.Kasashen yammaci na turai dai sun kakabawa gwamnatin Robbert Mugabe takunkumi,wadanda suka ce basu shafi alummomin kasar ba.

Shugaban kasar Tanzania,wanda kuma shine ke jagorantar wannan taro Jakaya Kikwete ya bayyana cewa,matsalolin siyasa dana tattalin arziki da Zimbabwen ta fada ciki,na bukatar wannan taro yayi mahawarori masu maana.