Taron shugabanin Majalisun dokokin ƙasashe masu anfani da halshen Portuganci | Labarai | DW | 10.07.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron shugabanin Majalisun dokokin ƙasashe masu anfani da halshen Portuganci

Shugabanin majalisun dokokin ƙasashe masu anfani da halshen Portuganci, sun buɗa zaman taro yau ,a birnin Lisbonne na ƙasar Portugal.

Baki ɗaya sun yi na´am, da girka wata ƙungiya, da za ta ƙunshi majalisun dokokin ƙasashen dunia, masu anfani da wannan halshe.

Ranar 17 ga watan da mu ke ciki za a bikun kaɗɗamar da wannan ƙungiyar, a kasar Guinee Bissao.

Babban yaunin da ya rataya kanta, shine na ƙarfafa mu´amila, demokradiya, da kuma cuɗe ni in cuɗe ka, tsakanin ƙasahe membobin ƙungiyar, sannan da shinfiɗa, dokokin bai ɗaya, ga al´ummomin ƙasashen.

Bikin kaɗɗamarwa ya yi daidai, da cikwan shekaru 10, da girka kungiyar CPLP da ta kunshi kasashen Portugal,Angola, Bresil, Cap-vert,Mozambique, Guinee Bissao, Sao-Tome da Timo ta gabas.