Taron shugabanin EU a Bruxelles | Labarai | DW | 09.03.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron shugabanin EU a Bruxelles

An shiga kwana na 2, a taron shugabanin ƙasashen ƙungiyar gamayya turai da aka fara jiya, a birnin Bruxelles na ƙasar Belgium.

Babban batun da ake ajendar taron a yinin yau,ya jiɓancin ɓullo da sabin hanyoyin mallakar makamashi don yaƙi da ɗumamar yanayi.

Shugabar gwamnatin Jamus da ahayin yanzu ke jagorantar EU ta bayyana sabanin ra´ayoyi da su ka sa tarnaki ga wannan batu a mahaurorin da su ka gudana jiya, saidai a cewar ta, akwai alamun cimma daidaito a kan batun.

A ɗaya hannun shugabanin sun tantana, a kann jaddawwalin bikin cikwan shekaru 50 da girka ƙungiyar taraya turai.

A nan ma, an fuskanci saɓanin ra´ayoyi a game da batun faɗaɗa wannan ƙungiya, da kuma hanyoyin cuɗe ni in-cuɗe ka, tsakanin ƙasashe 27 membobin ta.