1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron shugabanin EU a ƙasar Finlande

October 20, 2006
https://p.dw.com/p/BufG

Nan gaba ayau ne ,shugabanin ƙasashe, da na gwamnatocin ƙungiyar gamayya turai, za su gana a ƙasar Finlande, da ke riƙe da jagorancin karba –karba, na EU.

An shirya wannan haɗuwa ta mussamman, da zumar yin magana da murya ɗaya, kamin ganawar da za su yi, da shugaban ƙasar Russia, Vladmir poutine.

Babban batun da zai mamaye ajendar wannan taro, ya shafi makamashi, kasancewar ƙasar Russia, ke bada kashi 25 bisa 100 ,na jimmilar makamashin da kasashen EU ke anfani da shi.

A wasiƙar gayyata, da ya rubuwa shugabanin EU, praministan Finlande, mai masaukin baƙi, Martti Vanhanen, ya bukaci cimma matsaya ɗaya a game da yadda za su tunkara Vladmir Poutine.

An na samun saɓanin ra´ayoyi, tsakanin ƙasashe 25, na EU a kan wannan batu mai sarƙƙaƙiya.

A yayin da wasu, ke bukatar ƙulla dangantakar bai ɗaya da Russia, wasun na tunanin akasin haka.

A ɗaya wajen, shugabanin EU, za su anfani da wannan dama, domin tantana batutuwan da su ka jiɓancin demokradiya, da yancin faɗin albarkacin bakin yan jarida a Russia.