Taron shugabanin APEC a Sydney | Labarai | DW | 05.09.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron shugabanin APEC a Sydney

A birnin Sydney na ƙasar Australiya, shugabanin ƙasashe membobin ƙungiyar ci gaban yankunan Asia da na Pacific ,na cigaba da zaman taron su na shekara-shekara.

Shugabanin na anfani da wannan dama, domin yin bitar halin da a ke ciki a rayuwar ƙungiyar da kuma ayukan da ta gudanar ta fannin cimma bururukan da ta sa gaba.

Kazalika dama taron watza dama ce ta masanyar ra´ayoyi agame da al´amuran da ke wakana a a fagen siyasa da na diplomatia a dunia.

A yayin da ya gabatar da jawabi shugaban ƙasar Amurika Georges Bush, ya bayyana matsalar da ke ciwa Amurika tuwo a ƙwarya a halin yanzu, wato yaƙin Irak.

A cewar shugaba Bush, akwai ci gaba mai inganci ta fannin samar da zaman lahia a ƙasar ta Irak.

Kamin ya halarci taron na Sydney ,Bush ya kai ziyara ba zata a ƙasar Irak.

Shima Praminista mai masaukin baƙi John Haward, wanda ke ƙawance da Amurika a Irak, ya tabatar da cewar, dakarun Australiya ,za su ci gaba da zama Irak, kafaɗa da kafaɗa da sojojin Amurika, har lokacin da kwanciyar hankali ta tabbata.