1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron shugabanin ƙasashen larabawa a Ryad

Nan gaba a yau ne shugabanin ƙasashen larabawa, za su fara zaman taron yini 2 a birni Ryad na Saudi Arabia, domin masanyar ra´yoyi ,a game da hanyoyin warware rikicin da ke wakana a yankin gabas ta tsakiya.

Mahimman batutuwan da ke ajendar taron, sun haɗa da rikici tsakanin Isra´ila da Palestinu da yaƙin ƙasar Isra´ila da kuma batun makaman nuklear ƙasar Iran.

A dangane da rigimar Libanon, mahalarta taron, sun ƙudurci tantana ta, a sahu na 2, ta la´akari da rashin fahintar da aka samu, tsakanin magabatan ƙasar, wanda su ka halarci taron da tawagogi 2 masu gaba da juna.

Saidai a yayin da a ke ga, wannan taro,ya samu haɗin kai daga shugabanin ƙasashen larabawa baki ɗaya, shugaba Mohhamar Ƙhaddafi na Lybia, ya ƙaurace masa, domin a cewar sa, bai zai tsinana komai ba, illa kawai, ƙara raba kanun ƙasashen musulmi, da kuma aza karan tsana ga ƙasar Iran.

Sakataran harakokin wajen ƙungiyar gamayya turai Havier Solana, na daga tawagogin da su ka sauka birnin Ryad, ya kuma alƙawarta cewar, EU zata bada haɗin kai, ga sakamakon da taron zai cimma.