1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron shugabanin ƙasashen Afrika a birnin Ouagadougou

Shugabanin ƙasashen Afrika sun kammala zaman taron da su ka shirya birnin Ouagadougou na ƙasar Burkina Faso.

A tsawan yini 2, shugabanin sun tantana game da giɓi tsakanin Afrika da sauran ƙasashen dunia, a game da husa´o´in zamani ,na aiki da na´ura mai ƙwaƙƙwarwa.

Hukumar Majalisar Ɗinkin dunia mai kulla da ci gaban ƙasashe tare da haɗin ƙungiyar bankin ƙasashen Afrika su ka shirya wannan taro da zumar masanyar ra´ayoyi a tsakanin Afrika da ƙasashen da su ka ci gaba ta fannin husa´o´in zamani na anfani da na´ura ma kwakkwarwa da kuma Internet .

Mahaurorin da ka shirya, sun tabbatar da cewa, ƙasashen dunia sun yi wa Afrika fintikau a j kann wannan batu.

Shugabanin ƙasashe 3 da su ka hada Blaise Campoare na Burikina Faso da Thomas Yayi Boni na Benin da kuma Denis Sassou Nguesso na Congo su ka halarci wannan taro.

Kampanin Microsoft reshen Afrika, ya alkawarta bullo da wasu sabin dubaru, domin taimakawa Afrikawa su laƙanci aiki da wannan husa´o´i, da su ka kasance, riga zamani a saki a huta.