1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron shugabanin ƙasashen ƙungiyar Comesa.

Shugabanin ƙasashe ,da na gwamnatocin ƙungiyar tattalin arziki yakunan kudu, da gabacin Afrika,wato Comesa, sun buɗa zaman taron ƙoli na 11, a ƙasar Djiboutie.

Ajendar taron, ta ƙunshi mahimman batutuwa guda 2, wato shigi da ficin hajoji tsakanin su, da kuma rigingimmun da ke wakana a wasu daga cikin wannan ƙasashe.

A dangane da batu na farko, babban burin da su ke bukatar cimma, shine yaye shinge cinikaya ta hanyar sauƙƙaƙa awan kaya, a kan iyakokin ƙasashen Comesa, kamin nan da shekara ta 2008.

Ƙungiyar Comesa, da aka girka tun shekara ta 1993,na da cibiyar ta,a ƙasar Zambia, kuma ta ƙunshi kasashe 19 masu yawan al´ummomi milion ɗari 4.

Shugabanin ƙasashen za su anfani da wannan domin masanyar ra´ayoyi a game da rigingimun da ke gudana, a ƙasshen Sudan, Ethiopia, Erytrea, da Jamhuriya Demokradiyar Kondo, dukan su membobin ƙungiyar.

A ƙarshen tarton shugaban ƙasar Djiboutie, Isam´il Omar Guelley, zai ɗauki jagorancin Comesa na tsawan shekara ɗaya.