1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron shuagabannin Au

June 29, 2007

Yau ake bude taron shugabannin Au A Accra

https://p.dw.com/p/BtvB
Alpha Konare
Alpha KonareHoto: AP

A yau ne ake bude taron yini uku na shugabannin kasashen dake kungiyar gamayyar Afrika Au a birnin Accra,kasar Ghana,inda zaa yi nazari kan makomar wannan kungiya shekaru 5 bayan kafuwarta.

Bayan gazawar kungiyar gamayyar Afrika wajen samarda zaman lafiya a wuraren dake fama da rigingimu da suka hadar da Somalia da Lardin Darfur din kasar Sudan,anasaran Shugabannin kasashe da suka hadar da mai masaukin baki John Kufour da Moamer Gadhafi na Libya,zasu sake jaddada bukatar hadin kai tsakanin gamayyar kungiyar kasashen Afrikan,wanda shine hanya kadai da zaa cimma buri a wannan nahiya.

Tasron yini ukun dai zai mayar da hankali ne wajen tattauna makomar tarayyar Afrika,bayan kafa ta daga tsohuwar kungiyar hadin kan kasashen Afrikan a shekara ta 2002,kungiyar da kawo yanzu ta kasa haifar da da mai idanu.

gwamnatoci daga kasashe 53 dake da wakilci a kungiyar za s u tabka mahawara adangane matsalolin dake kawio jinkiri adangane da dakarun hadin gwiwa da suka alkawarta turawa zuwa kasar Somaliu,ikjg ua,a taron daya gudana a kasar Habasha,kana a hannu guda kuma da matsalar lardiun Darfur din kasar Suda -n dayaki ci yaki cinyewa.

Shugaban hukumar kungiyar ta AU Alpha Omar Konare ya fadawa taron sharan fagen ministocin harkokin ketare na kungiyar a jiya cewa,samarda madadin hadin kan kasashen,shine kadai madafa a kokarin da akeyi na ganin cewa an warware rigingimun wannan nahiya dake fama da talauci.

Shima shugaba John Kufour na Ghana ya sake nanata kalaman Shugaba Nkrumah wanda ya kirkiro wannan kungiya,nacewa babu yadda zaa cimma nasara ba tare da hadin kai ba.

Gazawan kungiyar ta Aui wajen tura dakaru zuwa birnin Mogadishu dai,sai na Uganda kadai dai,ya zame wani babban koma baya wa kungiyar.