Taron shekara shekara na jammiyar Labour a Birtania | Labarai | DW | 25.09.2006
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron shekara shekara na jammiyar Labour a Birtania

Ministan harkokin kudi na Britania,kuma mutumin da da akesaran zai gaji premier Tony Blair ,yace yayi nadamar irin fadan cikin gida dake gudana a jammiyarsu mai mulki ta Labour.Dayake jawabi wa taron sherkara shekara na jammiyar Labour,wanda ake ganin cewa,nan ne zai cika burinsa na gadar kujerar premier Britania,Gordon Brown ya yabawa Tony Blair a matsayin shugaba mai hangen nesa ,sai dai ya bayyana cewa akwai matsaloli na sabadin raayi a lokaci na tsawo na dangantakarsu.Ya bayyana cewa a shirye yake ya karbi ragamar shugabancin jammiyarsu ta Labour.Kawo yanzu dai Mr Blair bai sanar da ranar da zai sauka daga mukaminsa ba,sai dai yace wannan shine jawabinsa na karshe wa jammiyar Labour,a matsayinshi na shugabanta.

 • Kwanan wata 25.09.2006
 • Mawallafi Zainab A Mohammad
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bu5J
 • Kwanan wata 25.09.2006
 • Mawallafi Zainab A Mohammad
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bu5J