1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron shekara shekara na CDU

Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel ta buɗe taron kasa na yini biyu na jamiiyyar masu raayin mazan Jiya ta CDU a birnin Hanover.Jamiiyyar ta CDU dai na shirin amfani da wannan taro na shekara shekara wajen yin gyare gyare ,domin samun gindin zama a siyasar tarayyar jamus,tare da nisantar da kanta daga jamiiyyar masu sassaucin ra’ayi ta SPD,da suke mulkin haɗaka tare.Angela Merekel tace.“Wannan lokaci ne na mikewa tsaye,wanda ke nufin cewar daukaka tare da fadada manufofimmo,na inganta cigaban tarayyar Jamus.Adangane da hakane nake kira ga dukkan abokan tafiya a wannan yunkuri nacewar mun iso tsaki,ayanzu muna tsaki ,kuma dole ne mu zage Dantse.“