Taron shawarwarin sulhu na kungiyar yan tawayen SLM na yankin Dafur | Labarai | DW | 18.10.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron shawarwarin sulhu na kungiyar yan tawayen SLM na yankin Dafur

Kungiyar yan tawayen Dafur ta SLM a kasar Sudan ta ce tana shirin gudanar da babban taro domin sasantawa domin tsarwa kasar kykyawar makoma. Kungiyar tace daya daga cikin makasudin taron sasantawar shi ne dinke barakar dake tsakanin yayan ta. Kungiyar ta SLM tace taron wanda zai gudana a ranar 25 ga wannan watan zai sami halartar wakilai kimanin 800 daga sassan kasar. Bugu da kari tace an gaiyato baki yan kallo su kimanin 200 wadanda suka hada da wakilai daga Amurka da kungiyar tarayyar turai da Majalisar dinkin duniya da kungiyar gamaiyar Afrika da kuma yan siyasa da maluma na kasar Sudan. Tun da farko manazarta sun baiyana cewa rarrabuwar kawuna tsakanin kungiyoyin yan tawayen Dafur ka iya kawo jinkiri ga yunkurin kungiyar gamaiyar Afrika na warware rikicin yankin na Dafur. Kungiyar yan tawayen ta SLM ta rabu gida biyu inda shugaban kungiyar Abdulwahid Mohammed Nur yake jagorantar bangare daya, yayin da kuma sakataren kungiyar Mani Arko Minawi yake jagorantar daya bangaren. Kimanin mutane 180,000 zuwa 300,000 aka kiyasta sun rasa rayukan su a Dafur tun bayan da rikici ya barke a yankin a shekarar 2003, yayin da wasu fiye da miliyan biyu suka tagaiyara.