Taron share fage na ƙasashe masu kujerun dindindin a komitin sulhu, a kan rikicin nukleyar Iran | Labarai | DW | 09.03.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron share fage na ƙasashe masu kujerun dindindin a komitin sulhu, a kan rikicin nukleyar Iran

A birnin Vienna na kasar Austriya wakilai kasashen 35 membobi a hukumar yaƙi da yaɗuwar makaman nuklea sun yanke shawara gurfanar da Iran gaban komitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Dunia bayan shekaru 3 a na ka kai ruwa rana a kan matsalar makaman nuklea.

Jim kaɗan bayan bayana sakamakon taron, jikadodin kasashe 5, masu kujerun dindindin a komitin sulhu na Majalisar dinkin dunia, wato Amurika, Fransa, Rasha, Britani, da China sunyi zaman taron share fage a kan wannan batu mai sarƙƙaƙiya..

Jikadan ƙasar Chine ya bayyana cewar, wakilai ƙasashen a komitin sulhu, sun yi masanyar ra´ayoyi a kan yadda za su ɓullo ma al´amarin, da kuma samar da wata sabuwar mafita, ba tare da an kai ga ɗaukar matakan hukunci ba ga Iran.

Kamar yada su ka saba, ƙasashen China da Russie, na adawa da matakin hukunta Iran a kan wannan batu.