1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron sauyin yanayi

Shugabannin kasashe da dama za su gabatar da jawabai a taron sauyin yanayi da ke gudana a birnin Marrakesh na Moroko.

Shugabannin gwamnatocin kasashe da dama za su gabatar da jawabai a wajen taron sauyin yanayi da ke gudana a birnin Marrakesh na kasar Moroko.

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon ya shaida wa manema labarai a zauren taron cewa yana da karfi gwiwa zababben Shugaban Amirka Donald Trump ba zai dagula lamura ba bisa nasarorin da aka samu kan matakan dakile sauyin yanayi da duniya ke fuskanta.

Kimanin kasashen duniya 200 suke da wakilai a taron da aka fara ranar 8 ga wannan wata na Nowamba, wanda za a kammala umma'a mai zuwa da ke zama 18 ga watan na Nowamba.