Taron sasantawa da wanzar da zaman lafiya da tsaro a Iraqi | Siyasa | DW | 11.03.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Taron sasantawa da wanzar da zaman lafiya da tsaro a Iraqi

Manyan kasashe na masu fada aji tare da makwabtan Iraqi sun amince da yunkurin tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali a Iraqi

default

Shi dai wannan taro wanda ya hada da manyan kasashe masu karfin fada aji da suka hada da Amurka da Britaniya da Faransa da China da kuma Rasha tare da jakadu na majalisar dinkin duniya da kuma kasashe makwabtan Iraqi wadanda suka kunshi Iran da Syria da Bahrain Masar da Jordan da Kuwait da Turkiya da kuma Saudi Arabia, ya gudana salin Alin cikin nasara da kwanciyar hankali.

A karon farko a wannan taro wakilan Amurka sun zauna gaba da gaba da jamiai daga kasashen Iran da Syria domin tattauna yadda zaá shawo kan rikici dariku da kuma kyautata shaánin tsaro a kasar Iraqin da yaki ya yiwa kacaca.

Ministan harkokin wajen Iraqi Hoshiyar Zabari yace akwai matukar muhimmanci ga tattaunawa tsakanin Amurka da Britaniya da Iran da kuma Syria. Wannan dai shi ne taro irin sa na farko da ya gudana tun bayan da Amurka ta jagoranci mamayar Iraqi a shekarar 2003.

Ko da yake an yi musayar kalamai masu zafi tsakanin Amurka da kasar Iran wadanda basa ga maciji da juna, duk da haka taron ya yi armashi domin kuwa dukkanin su, sun amince cewa ba zai amfani kowa ba, idan Iraqi da alúmar ta suka cigaba da kasancewa cikin hali na kakanika yi.

Jakadan Amurka Zalmay Khalizad da jamián kasar Iraqi sun baiyana dole a dakatar da kwararar mayakan sa kai dake ketarowa da makamai daga kasashen Iran da Syria idan ana bukatar shirin sasantawa a tsakanin alúmomin Iraqi ya yi nasara.

Sai dai a yayin da shugaban Amurka George W Bush ya bada umarnin tura karin sojoji 4,400 zuwa Iraqi, a waje guda wakilan kasar Iran a taron sun baiyana cewa ingantacciyar hanya ta samun zaman lafiya a Iraqi ita ce janye daukacin sojin Amurka da kawayen ta daga Iraqi. Jakadun na Iran suka ce kasancewar Amurka a kasar Iraqi shi ne yake wanzar da kungiyoyin yan tarzoma da kuma suke amfani da wannan a matsayin hujja ta kai hare hare.

Bugu da kari Iran ta koka a game da yan kasar ta dake tsare a hannun Amurka bisa zargin cewa suna taimakawa ayyukan tarzoma a Iraqi, tana mai cewa jamián diplomasiya ne kuma ya kamata a sake su.

Jakadan Amurka a Iraqi Zalmay Khalizad ya yaba da tattaunawar data gudana tsakanin Amurka da wakilan kasar Iran. Yace tattaunawa da Iran da sauran kasashe a game da kasar Iraqi ta yi maána, ta kuma taállaka ga sulhunta matsalolin da aka shirya taron domin sa.

A nasa bangaren P/M Iraqi Nuri al-Maliki ya yi kira ga sauran kasashe a yankin mai arzikin mai su daina daurewa yan taádda gindin, su kuma yi bakin iyawar su wajen taimakawa zaman lafiya a Bagadaza. Yace abu ne mai muhimmanci ga kowa ya kare zubar da jini da hasarar rayuka a dukkan iyakokin Iraqi.

Shi ma da yake tsokaci Ministan harkokin wajen Iraqi Hoshiyar Zabari ya baiyana gamsuwa da taron wanda yace a dangane da batutuwan da aka tattauna a kan su, sun maida hankali ne kachokan a kan samun zaman lafiya a Iraqi, babu wata ajanda ta siyasa da aka gabatar. Yace taron yi armashi idan aka yi laákari da mutanen da suka halarci taron da kuma musayar raáyi da aka yi a tsakanin dukkan wakilan taron. An cimma kyakyawar nasara.

Hoshiyar zebari yace an kafa kwamitoci da suka hada da tsaro dana kula da yan gudun hijira da kwamitin kan arzikin mai da kuma rabon madafan iko. Wakilan taron sun amince za su sake haduwa a cikin watan Aprilu. Kasashen Jamus da Japan da Italiya da Kanada suma sun nuna shaáwar su ta halartar taron na gaba.