1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron sanin makomar Afghanistan

Umar Saleh SalehJuly 20, 2010

Ƙasashen duniya sun amince da shirin shugaba Karzai na sasantawa da 'yan Taliban

https://p.dw.com/p/OQ3E
Hoto: DW

Sanarwar bayan taron da ƙasashen duniya suka yi akan samar da zaman lafiya a ƙasar Afghanistan, ya yaba da shirin sulhun da shugaba Karzai ya ɓullo da shi tare da 'yan ƙungiyar Taliban ɗin da suka amince su ajiye makaman su, kana su taimaka wajen sake gina ƙasar.

A jawabin rufe taron sanin makomar Afghanistan da ya yi, shugaba Hamid Karzai ya bayyana cewar, ƙasar sa na da ƙudurin karɓar alhakin tsaron ta nan da shekara ta 2014. Shugaban, wanda ya gana da wakilai daga ƙasashe 70 na duniya ciki harda ministocin kula da harkokin wajen ƙasashe 40 a birnin Kabul, fadar gwamnatin ƙasar Afghanistan, ya bayyana muhimmancin tattaunawar da suka gudanar, wadda ta mayar da hankali akan samar da zaman lafiya a ƙasar.

Babban sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya Ban Ki Moon wanda ke cikin waɗanda suka jagoranci taron ya ce taron ya cimma manufar gudanar da shi, inda kuma ya ce a shirye Majalisar take ta taka rawar data dace wajen mayar da ƙasar a bisa kyakkyawar turba:

" Majalisar Ɗinkin Duniya da ni kaina, zamu yi dukkan mai yiwuwa domin taimakawa samar da kyakkyawar makoma gareku - 'yan Afghanistan da kuma 'ya'yan ku. Masu girma ministocin dake halartar wannan taron, al'ummar Afghanistan na yi mana fatan alheri a wannan taron, amma za su yanke shawara ce bisa la'akari da ayyukan da muka yi, ba wai abubuwan da muka furta ba."

A halin da ake ciki kuma sakatare janar na ƙungiyar ƙawancen tsaron NATO Anders Foghs Rusmussen, ya bayyana cewar, duk wata janyewar da sojojin ƙasa da ƙasar da za su yi, za ta dogara ne akan irin ci gaban da aka samu a ƙasa ta fuskar kyautatuwar sha'anin tsaro, ba wai ajiye wani wa'adi ba.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh

Edita : Umaru Aliyu