1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron sake gina Pakistan

October 15, 2010

Ƙungiyar Tarayyar Turai(EU) ta yi taron duba hanyoyin sake gina Pakistan

https://p.dw.com/p/PfC9
Tutocin EU da PakistanHoto: DW

Wakilai gun wata tattaunawa da Ƙungiyar Tarayyar Turai ta gudanar a birnin Brussels na ƙasar Belijyam, domin duba hanyoyin sake gina ƙasar Pakistan, bayan bala'in ambaliyar ruwan da ya rutsa da ita, sun yi kira ga ƙasar ta Pakistan da ta gaggauta yin wasu gyare -gyare. Ministan harkokin wajen Pakistan, Shah Mehmood Qureshi ya amince da sukan da aka yi wa ƙasarsa game da tsarinta na karɓar haraji, inda ya ce gwamnati na ɗaukar matakan yin gyara game da haka. Rukunin ƙasashen da ke kiran kansu ƙawayen Pakistan su guda 26, da suka haɗa da Japan, da Kanada da Jamus da Bankin Ci gaban Nahiyar Asiya, na daga cikin waɗanda suka shiga tattaunawar. Ministan harkokin wajen Jamus, Guido Westerwelle ya ce yana kyautata fatan samun shugabanci na gari da kuma dimukuraɗiya a Pakistan. A dai halin da ake ciki yanzu wasu kafafe da ke da alaƙa da ma'aikatar tsaron Pakistan sun ce wasu mutane uku sun rasa rayukansu sakamakon harin da wani jirgin saman Amirka mai sarrafa kanshi ya kai a arewacin yankin Waziristan da ke kusa da iyakar ƙasar da Afganistan, wanda maƙarfafa ne ga 'yan Taliban da Al-Ƙa'ida.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas

Edita: Abdullahi Tanko Bala