Taron Sakatare-Janar Na MDD Da Manema Labarai | Siyasa | DW | 22.12.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Taron Sakatare-Janar Na MDD Da Manema Labarai

Babban abin da ke ci wa 'yan jarida tuwo a kwarya a duk lokacin da suka sadu da Kofi Annan a 'yan kwanakin baya-bayan nan shi ne zargin almundahana da ake yayatawa a shirin MDD na cinikin mai domin sayen abinci ga kasar Iraki

Sakatare-Janar na MDD Kofi Annan

Sakatare-Janar na MDD Kofi Annan

Ainifin manufar taron na manema labarai shi ne waiwayar baya a game da abubuwan da suka faru a wannan shekarar mai karewa da kuma shirye-shiryen garambawul da ake yi ga tsare-tsaren MDD a shekara mai kamawa ta 2005. Amma a kwanakin baya-bayan nan wasu batutuwa ne dabam ke ci wa ‚yan jarida tuwo a kwarya a duk lokacin da suka fuskanci sakatare-janar Kofi Annan da tambayoyi sakamakon farfagandar da jami’ai da kuma kafofin yada labaran Amurka ke yayatawa, lamarin kuma dake dada jefa Kofi Annan cikin mawuyacin hali na kaka-nika-yi. A lokacin da yake amsa tambayar da aka yi masa a game da murabus sakatare-janar din cewa yayi:

Dangane da murabus dai a wannan marra da muke ciki yanzun wannan magana ba ta taso ba saboda akwai ayyuka masu yawa a gabana. Ina da cikakken goyan baya daga sauran kasashen MDD kuma zamu ci gaba da hadin kai domin magance matsalolin dake gabanmu.

Sakatare-janar Kofi Annan ya kara da bayanin shirinsa na bin bahasin zargin almundahana da ake yi ganin yadda wannan tabargaza ke neman bata sunansa da na majalisar baki daya. Ya ce nan da karshen watan janairu mai zuwa ne za a samu sakamakon farko na kwamitin bin-bahasin da ya nada domin binciko ainifin gaskiyar abin da ya faru a game da shirin MDD na cinikin mai domin sayen abinci ga kasar Iraki. Kofi Annan ya kara da cewar:

Wannan shekarar mai karewa ta kasance mai muni da wahala kuma ina farin cikin ganin ta kawo karshenta. An samu wasu dake kalubalanta ta da ita kanta MDD, amma ba zamu saduda ba, zamu yi bakin kokarinmu wajen bin diddigin dukkan zargin da ake mana.

Daya matsalar kuma ita ce garambawul da ake da niyyar aiwatarwa ga MDD a daidai lokacin da take bikin samun shekaru 60 da kafuwa. A lokacin da yake nuni da haka Kofi Annan yayi tsokaci a game da dukufar da aka yi kacokam akan neman karin wakilcin kasashe a kwamitin sulhu na MDD. Ya ce daga baya-bayan nan kwararrun masana suka gabatar da wani kundin dake dauke da shawarwari 101, wadanda gaba daya suka shafi kafofi dabam-dabam na majalisar, ba wai kawai kwamitinta na sulhu kadai ba. Amma babban abin da yake fata dangane da shekara mai kamawa ta 2005 shi ne samun ci gaba a fafutukar kawo karshen rikice-rikicen da ake fama da su a Iraki da Sudan, inda ake fama da salwantar rayukan mutanen da ba su san hawa ba su san sauka ba.