1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron rage makaman nukiliya

April 12, 2010

Kimanin shugabannin ƙasashe 47 ne ke halartar taron na yini biyu a Washington

https://p.dw.com/p/MuXt
Adawa da makaman nukiliyaHoto: AP Graphics

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta ce za ta matsa ƙaimi a gun taron ƙoli kan makaman nukiliya a Amirka, domin a tsaurara matakan kariya daga yaɗuwar sinadaran da ake amfani da su wajen harhaɗa makaman nukiliya. Jim kaɗan kafin ta tashi zuwa birnin Washington, Merkel ta faɗawa manema labarai a Berlin cewa babbar barazana a nan ita ce ƙungiyoyin 'yan ta'adda kamar Al-Qaida ka iya samun sinadaran ta ɓarauniyar hanya domin amfani da su a matsayin makaman ƙare dangi.

"Barazanar da muke fuskanta a wannan ƙarni na 21 sun haɗa da ƙungiyoyin 'yan ta'adda kamar su Al-Qaida waɗanda bai kamata sinadaran da za a iya ƙera makaman nukiliya da su, su shiga hannunsu ba. Domin haka na nufin ƙarin haɗari a kanmu ne."

Shi ma shugaban Amirka Barak Obama ya yi irin wannan furucin. Muhimmin batun da zai ɗauki hankalin shugabannin ƙasashe kimanin 47 da za su halarci taron na yini biyu, shi ne hana yaɗuwar makamai da sinadaran makamin nukiliya. A taron kuma za a tattauna akan shirin nukiliyar ƙasar Iran da ake taƙaddama kansa.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal

Edita: Yahouza Sadissou Madobi