Taron PLO a Rammallah | Labarai | DW | 20.06.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron PLO a Rammallah

Komitin zartaswa na ƙungiyar PLO ya buda zaman taro a Rammallah bisa jagoranci shugaban Mahamud Abbas.

A tsawan yini 2 mahalarta wanan taro za su tantana a game da halin da Palestinu ta tsisnta kanta a ciki ,bayan da ƙungiyar Hamas ta mamaye zirin Gaza.

A cewar minsitan watsa labarai na sabuwar gwamnatin da aka girka, wato Ryad Al Maliki, shugaba Mahamud Abbas ya bayyana bukatar hukumar zartaswa ta ƙungiyar PLO ta maye gurbin Majalisar dokoki a matakin wucin gadi.

Sanarwar ƙarshen taro za ta bayana shawara da a ka yanke a game da wannan batu.

A halin da ake ciki dai Praministan Salam Fayyad na ta samun goyan baya daga sassa daban-daban na dunia.

A hurucin da yayi a game da rikicin na Palestinu, shugaban ƙungiyar haɗin kan ƙasashen Jamus da Isra´ila

Johannes Gester, cewa ya yi yanayin da ke wakana a Palestinu, dama ce ta samar da zaman lahia.