1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron Paris a kan rikicin Darfur

June 24, 2007
https://p.dw.com/p/BuHy

Sakaratiyar harakokin wajen Amurika Condoleesa Rice, ta sauka a birnin Paris na ƙasar France, inda zata halarci taron ƙasa da ƙasa a game da rikicin yankin Darfur na ƙasar Sudan.

France ta gayyaci wannan taro gobe, domin gudanar da mahaurori, a game da mattakan kawo ƙareshen rikicin Darfur, da kuma na kai talafin ggagawa ga yan gudun hijira.

Condoleesa Rice, ta yaba faɗi ka tashin da France ke yi ,ta fannin samun masalaha a rikicin Darfur.

A ganawar da ta yi yammacin yau, da takwaran ta na France Bernard Kouchner, sun yi masanyar ra´ayoyi a game da manufofin France, na kai agaji ga yan gudun hiira Darfur, ta hanyar zirin sararin samaniya.

Rici ta yi kira ga hukumomin Khartum, su cika alƙawarin da su ka ɗauka, na amincewa da tura tawagar majalisar Dinkin Dunia, domin shiga tsakanin a rikicin.

Taron na ƙasar France da zai fara gobe , idan Allah ya kai mu zai samu halartar wakilan Majalisar Ɗinkin Dunia , da na ƙungiyar gamayya turai, kazalika ƙasashen Sin , Russie, da Japon sun tuwa tawagogin su.