Taron Papa Roma da jakadun ƙasashen musulmi a Castelgandolfo. | Zamantakewa | DW | 25.09.2006
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Taron Papa Roma da jakadun ƙasashen musulmi a Castelgandolfo.

A yunƙurin ɗinke ɓarakar da aka samu tsakanin daular Vatican da duniyar musulmi, sakamakon wata katoɓarar da Papa Roma Benedikt na 16 ya yi, a wata laccar da ya bayar a jami'ar Regensburg, a ziyarar da ya kawo a nan Jamus, daular ta Vatican ta gayyaci jakadun ƙasashen musulmi zuwa wani taro a fadar bazara ta Papa Roman da ke Castelgandolfo.

Papa Roma da wakilan ƙasashen musulmi a zauren taron a fadar Castelgandolfo.

Papa Roma da wakilan ƙasashen musulmi a zauren taron a fadar Castelgandolfo.

A taron da Papa Roma Benedikt na 16 ya yi yau da jakadun ƙasashen musulmi da ke da hulɗa da daular Vatican, za a iya lura da cewa, a duk tsawon lokacin da yake jawabi a ƙame yake. Hakan kuwa na nuna damuwarsa ne game da ɓacin ran da laccarsa a jami’ar Regensburg a nan Jamus ya janyo ga duniyar musulmi. Shugaban ɗariƙar Katolikan dai bai saki jiki ba, sai bayan jawabinsa da kuma taɓin da wakilan ƙasashen musulmin suka yi masa.

A cikin jawabin nasa, Papa Roma ya yi kira ga haɗin kai tsakanin kirista da musulmi don gina abin da ya kira wata gada ta lumana. Game da wannan burin dai, shugaban ɗariƙar Katolikan ya yi matashiya da wani jawabin da ya yi a shekarar bara, a taron matasan Katolika na duniya nan da aka yi abirnin Kwalan a nan Jamus:-

„Kamar yadda na nanata a Kwalan a shekarar bara, ba za a iya taƙaita tuntuɓar juna a huskar addini da al’adu tsakanin kirista da musulmi, a kan halin da muke ciki yanzu kawai ba. Wannan wani muhimmin jigo ne da ke da matuƙar muhimmanci a halin rayuwarmu, wanda kuma makomkarmu ta dogara a galibi a kai.“

Ba za a iya dai cim ma nasara a wannan fafutukar ba, inji Papa Roman, sai duk ɓangarorin biyu sun ba da ta su gudummowa. Kamata ya yi a sami girmama juna tsakanin ɓangarorin biyu, musamman a kan batutuwan da suka shafi ’yancin walwala wajen tafiyad da harkokin addini. Game da laccarsa, wadda ta janyo hauhawar tsamari tsakanin Vatican da duniyar musulmi kuwa, Papa Roman ya bayyana cewa:-

„Kowa dai na sane da dalilin kiran wannan taron yau. A makon da ya gabata ma, na sammi damar takalo wannan batun. A wannan taro na musamman yau kuma, ina son in nanata mutunta da kuma girmamawar da nake yi wa mabiya addinin islama.“

Jakadun ƙasashen musulmi 22 ne suka amsa gayyatar da Papa Roman ya yi musu zuwa fadarsa ta bazara ta Castelgandolfo, a cikinsu har da na ƙasashen Masar, da Iran, da Turkiyya, da Pakistan, da Libiya, da Indonesiya da kuma Siriya. Sai daga baya-bayan nan ne dai gwamnatin birnin Damascus ta amince da tura wakilinta zuwa taron. Bisa wani labarin da kafofin yaɗa labaran Italiyan suka buga dai, ƙasar Sudan ce kawai ƙasar musulmi mai hulɗa da Vatican, wadda ba ta tura wakilinta ba. A ɓangaren Papa Roman dai, taron ya ci nasara, kuma ya cim ma burinsa, ta sanya alamar cewa, a shirye ƙasashen musulmi suke su amsa gayyatar da ya yi musu na shiga taroon tuntuɓar juna.

 • Kwanan wata 25.09.2006
 • Mawallafi YAHAYA AHMED
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvTJ
 • Kwanan wata 25.09.2006
 • Mawallafi YAHAYA AHMED
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvTJ