Taron neman taimako ga Libanon a birnin Stockolm | Labarai | DW | 31.08.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron neman taimako ga Libanon a birnin Stockolm

Nan gaba a yau ne ƙasashe masu da hannu da shuni, da ƙungiyoyin bada agaji na ƙasa da ƙasa ke buɗa zaman taro, a birnin Stockolm na Sweeden, da zumar samar a kuɗaɗen sake gina ƙasar Libanon, da hare haren Isra´ila su ka yi kaca kaca da ita.

Praministan Libanon Fouad Siniora, zai anfani da wannan dama, domin jaddada kira zuwa ƙasashen dunia, a kan wajibcin hidda Libanan daga uƙubar karya tattalin arziki da ta tsinci kanta a ciki.

Burin da ake buƙatar cimma, a wannan taro, shine na tattara kuɗaɗe da yawan su, ya tashi dalla milion ɗari 5.

Tuni ƙungiyar gamayya turai ,ta alƙawarta taimakawa da dalla milion 42.

A halin da ake ciki jimmilar tallafin da EU ta bada, ya tashi dalla milion100, domin sake gina Libanon.