1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron musulmi a Jamus.

May 12, 2010

Barazanar ƙaurace wa taron musulmi a Jamus.

https://p.dw.com/p/NMUE
Ginin masallaci a Turai.Hoto: DW

Wata ƙungiyar musulmi da ke zaman ta biyu mafi girma a nan Jamus ta ba da sanarwar ƙaurace wa wani taron musulmi da gwamnatin Jamus za ta ɗauki ɗawainiyar gudanar da shi a birinin Berlin a mako mai zuwa. Ƙungiyar mai suna Central Council of Muslims da ke wakilitar ƙawancen masallatai na 'yan Sunni a faɗin Jamus ta ce tattaunawar ba ta ba da muhimmaci ga buƙatar taɓo ƙyamar da ake nuna wa muslunci yayin taron ba kuma taro na zaman wani abu da gwamnati ta ƙaƙaba gudanar da shi ba da wata takamammiyar manufa ba. Tun watanni biyu da suka gabata ne kuma wata babbar ƙungiya da kuma ke wakilitan musulmi da mafi yawansu Turkawa ne, ta janye daga wannan taro domin nuna zumunci ga wani mambanta da ake gudanar da bincike akansa bisa laifin kauce wa biyan haraji, halalta kuɗin haramu da kuma kafa gungun 'yan ta kife. Taron zai mai da hankali ne akan buƙatar sajewar musulmi kimanin miliyan huɗu da ke zaune a Jamus.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas

Edita: Ahmed Tijani Lawal