Taron murar tsuntsaye a Brusels | Labarai | DW | 21.02.2006
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron murar tsuntsaye a Brusels

EU

Tawagar kwararrun jamian kula da lafiyar dabbobi na kungiyar gamayyar turai na gudanar da taro a birnin Brussels din kasar Belgium,domin tattauna yiwuwan daukan matakai na gudanar da alluran riga kafin mura wa tsuntsaya.Kasashen Faransa da Netherlands dai sun amince dayin hakan,ayayinda hukumar gudanarwa na kungiyar ta EU da sauran wakilan kasashe suka nuna adawa dayin hakan.Ministan harkokin gona na jamus Horst Seehofer da sauran jamiai sun nemi sanin tasirin wannan alluran riga kafi.A nasu raayi,yin hakan zai bukaci kudade masu yawa ,tunda dole ayiwa tsuntsayen wadannan allurai akalla sau 2 cikin tsukin makonni 3.

 • Kwanan wata 21.02.2006
 • Mawallafi Zainab A Mohammad
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bu7j
 • Kwanan wata 21.02.2006
 • Mawallafi Zainab A Mohammad
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bu7j