1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron muhalli na birnin Cancun

December 6, 2010

Jamus ta ce babu alamar cimma nasara a taron sauyin yanayin da ke gudana a ƙasar Mexico.

https://p.dw.com/p/QQnC
Ministan muhalli a Jamus Norbert Röttgen a lokacin wani taron manema labarai akan makamashi a birnin BerlinHoto: picte

Ministan kula da harkokin muhall a Jamus Norbert Röttgen ya bayyana cewar bai yi amannar za'a sami wani ci gaba mai ma'ana ba a taron da ƙasashen Duniya ke yi game da sauyin yanayi a birnin Cancun na ƙasar Mexico. A lokacin da yake yin jawabi ta wata tashar rediyo anan Jamus ministan ya ce maimakon ƙoƙarin cimma matsaya guda akan batun matsalar sauyin yanayi, kamata ya yi a mayar da hankali ga ɗaukar ƙananan matakai - amma ba na tilas ba wajen aiwatar da yarjeniyoyin da aka cimma a taron birnin Copenhagen na ƙasar Denmark.

A cewar ministan kula da harkokin muhalli na Jamus Norbert Röttgen babban burin da aka sanya a gaba shi ne rage ɗumamar yanayin da Duniya ke fama da ita ya zuwa marki biyu, tare kuma da ci gaba na ɗaukar matakan rage hayaƙin da masana'antu ke fitarwa. Ya ce tuni Jamus ta yi namijin ƙoƙari wajen zama abar koyi ta wannan fuskar.

Wakilai daga ƙasashen Duniya daban daban guda 190 ne ke ci gaba da gudanar da taro a birnin Cancun na ƙasar Mexico da nufin ɗaukar matakan shawo kan matsalar ɗumamar yanayi a duniya.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh

Edita : Halima Balaraba Abbas