1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron ministocin waje na kungiyar tsaro da mu´amila ta turai da yankin tsakiya Asia

December 5, 2005
https://p.dw.com/p/BvHo

Ministocin harakokin waje na kungiyar tsaro da mu´amila, ta kasashe turai da yankin tsakiyar Asia sun buda zaman taron shekara ta kasashe, a birnin Ljubljana na kasar Slovenia, bisa jagoranci shugaban kasar Dimitrij Ruppel.

A jawabin da yayi, shugaban ya bayyana ci gaban da a ka samu, tun taron Helsenki na shekara ta 1975, mussaman a game da girka demokradiyya, a kasashen da su ka balle daga tarraya Soviet.

Ministan harakokin wajen Sloveniya a jawabinsa ya maida himma a kan matsalolin da har yanzu ke mayar da hannun agogo baya ga nasarorin da kungioyar jke bukatar cimma.

A dangane da zaben shugaban kasa da ya wakana ranar jiya, a kasar Uzbekistan, da ya baiwa shugaban mai ci Nursultan Nazerbaiv dammar yin tazarce, mahalarta taron sun bayyana rashin amincewa da makudin da a ka tabka .

Saidai an samu rabuwar kanu tsakanin su, a yayin da wasu kasashen da su ka hada da Rasha, har sun aika da sakwanin taya murna ga saban shugaban.

Masu kulla da al´ammura na hasashen cewa, bisa dukkan alamu, za a samu rashin jituwa, ga sanarwar karshen taro da za a bayyana gobe idan Allah ya kai mu.