Taron ministocin waje na EU | Labarai | DW | 15.10.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron ministocin waje na EU

Portugal dake shugabantar kungiyar tarayyar turaia a yanzu,tayi kira ga ministocin harkokin wajen kungiyar dake gudanar da taro a Luxenburgh,dasu gaggauta zartar da matsayinsu kann sabon kudurin sauyi na wakilan kasahe 27 dake kungiyar,kafin taron da zaa gudanar a ranar alohamis a birnin Lisbon.Portugal wadda ke gudanar da zabe a ranar 21 ga wannan wata na okotoba,na bukatar ganin an samar da tsari guda na harkokin zabe a tsakanin kasashen,wanda zai iya bawa EU ikon zartar da hukunci akan karamar kasa,data nuna adawa.Ministan harkokin wajen Portugal Luis Amado,yayi fata cewar kafin faduwar ranar yau,ministocin zasu cimma matsaya guda.