Taron ministocin tsaro na EU | Labarai | DW | 01.03.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron ministocin tsaro na EU

Ministocin tsaro, na ƙungiyar gamaya turai na ci gaba da zaman taro a birnin Wiesbaden na yammacin Jamus.

A tswan yini 2 za su tantana batutuwa daban-daban da su ka shafi harakokin tsaro a ƙasashen yankin balkan da kuma Bosnia- Herzegovina, inda ƙungiyar EU ta yanke shawara rage yawan dakarun ta, da kimanin sojoji dubu 6.

A halin da a ke ciki, Bosnia ta girka sabuwar gwamnati, da kuma rundunar tsaro, ta ƙasa, a game da haka ya zama wajibi, EU ta janye dakarun ta, inji babban habsan sojojin ƙungiyar taraya turai, a Bosnia- Herzegovina, Jannar Jean-Paul Perruche.

A ɗaya wajen, ministocin tsaron ƙungiyar gamaya turai, za su tantata batun yancin Kosovo.

Da zaran wannan yanci ya tabatta, EU ta alkawarta aika runduna, wadda zata cenji dakarun Majalisar Ɗinkin Dunia.