Taron ministocin tsaro na ƙungiyar NATO a Netherlands | Labarai | DW | 24.10.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron ministocin tsaro na ƙungiyar NATO a Netherlands

Tabarbarewar halin tsaro da kuma kutsen da ´yan tawaye ke yi a Afghanistan shi ya fi daukar hankali a taron ministocin tsaron kungiyar kawance ta NATO dake gudana a kasar NL. Kasashen Amirka da Birtaniya na matsawa kawayensu na Turai lamba da su ba da karin dakaru da kayan aiki a yakin da ake yi ´yan tawayen Taliban a Afghanistan to amma majiyoyin kungiyar sun nunar da cewa kasashen biyu ba zasu samu yadda suke so ba. Ministocin na kuma tattaunawa akan shirin Amirka na kafa sansanonin kandagarkin makamai masu linzami a kasar Poland da Janhuriyar Czeck.