Taron ministocin suhuri na kungiyar EU a Brussels | Labarai | DW | 05.12.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron ministocin suhuri na kungiyar EU a Brussels

Ministocin suhuri na kungiyar taraya turai , sun kammala zaman taro, sahiyar yau, a birnin Bruxelles na Belgium.

Bayan mahaurorin da su ka tapka ministocin sun cimma matsaya daya, ta hido da rijistan kampanonin jiragen sama wanda sam, za a haramtawa jiragen su, shawagi a sararin samaniyar trurai.

Sun dauki wannan mataki domin yaki da yawan hadarurukan jiragen sama, da a watanin baya, su ka hadasa mutuwar mutane da dama.

Ministocin za su zayyana sharuda, da cilas ,sai kampani ya cika su, kamin ya samu amincewar kasashe turai baki daya, na saukar jirgen sa.