1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Taron ministocin NATO a Brussels

Mahawarar ministocin NATO kan sabbin wakilan ƙasashe

default

Ministan harkokin wajen Jamus ,Frank-Walter Steinmeier t

Shigar da sabbin wakilai daga yankin Balkan da gabashin Turai zuwa cikin kun ƙungiyar tsaro ta NATO,da halin da ake ciki a kasar Afganistan,sune muhimman batutuwa biyu da suka mamaye zauren taron ministocin harkokin wajen NATOn daya gudana a jiya abirnin Brussels.

Duk dacewar makonni kalilan ya rage a gudanar da babban taron kasashe 26 dake da wakilci a ƙungiyar Tsaron ta NATO,taron na jiya ya kasa cimma matsaya guda dangane da makomar sabbin kasashen dake neman shiga.

Akwai batutuwa masu sarkakkiyyar gaske na siyasa da tsaro da zasu cikanta dangane Kasashen yankin Balkan da suka haɗar da Kroshiya da Albaniya da Macedoniya ,wadanda ke neman shiga wannan ƙungiyar.A hannu guda kuma ga takaddama dake tsakanin Girka dake zama member a NATO da Macedoniya,wanda hakan ya jefa wannan batu cikin wani wadi na tsaka mai wuya,kamar yadda ministan harkokin wajen jamus Frank-Walter Steinmeier ya faɗi.

"Ina fatan za a amince da karɓan dukakkin ƙasashen uku.Sai dai Idan har aka samu saɓani dangane da dukkanin sunayen da aka gabatar,to ta hakan ne kadai zaa iya fuskantar matsala.Amma saboda bukatrn cimma matsaya guda,ya zamanto wajibi mu ji ra ayin Girka domin akada ya harfar da wata matsala tsakanimmu"

Yadai zamanto wajibi a cimma warware rikicin dake tsakanin Girka da Mazedoniya kafin lokacin taron na NATO dazai gudana a afarkon watan Afrilu,wanda hakan ne kadai zai kare Macedoniya daga fuskantar matsala da neman wakilci a kungiyar tsaron ta NATO.

Babban sakataren ƙungiyar ta NATO Jaap de Hoop Scheffer ya ce amincewa da waɗannan kasashe na turai cikin wannan kugiya da sauran masu bukata yana da matukar muhimmanci wajen ayyukan tabbatar da tsaro...

"Haɗewar ƙasashen yankin na turai a wannan kungiyar tsareo ta atalantika ,bamu sana abunda zai haifar daga karshe ba,domin hadewar su wani sinadari ne na zaman lafiya da tsaro"

A nata ɓangaren sakatariyar harkokin wajen Amurka Condoleeza Rice tace ya zamanto wajibi a acimma matsaya guda dangane da ƙasashen yankin gabashin na turai,domin sanin irin matsayi da zaa dauka a yayin taron da zasu gudanar a Bucharest.Sai dai acewartar kofar wannan kungiyata NATo buɗe take wa sabbin wakilai .

"A wannan ɓangaren babu cikakkun bayanai dangane da ƙasashen kan irin shirin da sukayi na daukar duk wani nauyi da zaa dora musu ,bisa ga yarjejeniyawa da wakilan NATO zasu cimmawa.Kuma zamu cigaba da tattauna wannan batu da sauran batutuwa da suka shafi kungiyar kafin taron mu na Birnin Buchares"