Taron ministocin mahhali a Postdam
March 16, 2007Talla
Idan an jimma kaɗan ne, ministocin kare mahhalli na ƙasashen G 8, tare da takwarorin su na Sin, India, Brazil Mexique, da Afrika ta Kudu, za su fara wani mahimin zaman taro a birnin Postdam dake kussa da Berlin a nan kasar Jamus.
A tsawanyini 2, ministocin za su masanyar raáyoyi a a game da hanyoyin kare gurgusuwar hamada, da dumamar yanayi, a fadin dunia baki daya.
Kazalika taronna matsayin share fage, ga babr haduwar shugababin kasashe masu karfin tatalin arziki da zata gudana a nan Jamus, a watan Juni na wannan shekara.
Babban burin da a ka sa gaba, shine na samun hadinkai daga wasu kasashe maus fada aji ,wanda har yanzu, su ka amincewa da rattaba hannu a kann dokar rage fida hayaƙin iskan gaz, wanda shine ummal iba ´sar ɗumamar yanayi.