Taron Ministocin kuɗin EU a Brussels | Siyasa | DW | 18.05.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Taron Ministocin kuɗin EU a Brussels

Ministocin kuɗin ƙasashe membobin ƙungiyar Tarayyar Turai na faɗi tashi domin kare darajar kuɗin EURO

default

Euro ya shiga cikin barazanar kariyar daraja

Ministocin kuɗin ƙasashen Ƙungiyar Tarayya Turai, sun sake zaman taro na mussamman jiya a birnin Brussels, da zumar lalubo hanyoyin  tsamo takardar kuɗin EURO daga kariyar darajar da ta samu kanta ciki.

A ´yan kwanaki baya bayan nan, taro  na bin taro shugabanin ƙasashe ko na gwamnatocin da kuma ministocin kuɗin ƙasashe membobin Ƙungiyar Tarayyar Turai sun shirya zama iri-iri da zumar cimma nasara taka birki ga kariyar tattalin arzikin da ta rusta ko kuma take shirin rutsawa da wasu ƙasashe daga cikinsu.

A wani mataki na "idan gemun ɗan uwanka ya kama da wuta shafa ma naka ruwa"ministocin kuɗin a zaman taronsu na jiya, a birnin Brussels sun jaddada buƙatar ganin ko wace ƙasa memba a EU,ta tsaurara matakan bunƙasa tattalin arziki kamar yadda ministan kuɗin Jamus Wolfgang Schäuble yayi bayani:

Ya zama wajibi gare mu mu rage yawan giɓin tattalin arzikin ƙasashenmu, ya zama wajibi gare mu, mu mutunta yarjejeniyar bunƙasar tattalin arzikin da muka rattaba ma hannu.Dole ne mu duka mu cikka wannan sharaɗi.

Shi kuwa saban ministan kuɗin Britaniya amfani yayi da wannan dama, inda yayi kira ga hukumar zartaswa ta Ƙungiyar Tarayya Turai ta rage yawan kuɗin da ta tsara kashewa a wannan shekara ta 2011.

Hakan zai zama kyakkyawan misali ga sauran ƙasashen EU.George Osborne yayi suka da kakkausar halshe ga matakin  hukumar zartaswa ta EU na ƙara yawan kuɗaɗen aiki da albnashin ma´aikatanta da kashi kussan shida cikin ɗari, a yayin da a hannu guda take matsa ƙaimi ga ƙasashe kamar su Girka, Spain, Portugal, da sauran su, su tsuke bakin aljihunsu.

Taron ministocin ya bayyana aniyar ɗaukar matakai masu ƙwari domin kare darajar Euro inji ministan kuɗin Luxemburg LUC Frieden:
Ko wace kasa wadda ke amfani da takardar kuɗin Euro zata yi iya kokari domin kare martabar Euro daga sharrin dillalai masu haddasi ruɗani cikin kasuwani domin cimma kazamar riba.Hakan na nufin kara sa ido ga harakokin kuɗin ƙasahse hasali ma wandsa ke cikin halin buƙatar tallafi.

A game da wannan batu na tallafi ministocin sun bada sanrawar cika alƙawarin da suka ɗauka na taimakawa Girka da ta faɗa halin tsaka mai wuya.A jiya talata, EU ta zuba tsabar  kuɗi dala miliya dubu 14 da rabi ga ƙasar Girka.Jamus ta zuba kashi ɗaya cikin huɗu na wannan kuɗaɗe.

Mawwallafi: Yahouza Sadissou Madobi Ediota: Ahmed Tijani Lawal