1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron Ministocin harkokin wajen Turai

Zainab MohammedNovember 19, 2007
https://p.dw.com/p/CJGD

Ministocin harkokin waje na kungiyar tarayyar Turai Eu sunyi kira ga sabon prime ministan da za’a naɗa a kosovo nan gaba,da kada ya gaggauta shailar yancin kann yankin daga Serbia.Babban jami’in dake kula da harkokin ketare na ƙungiyar Javier Solana yace har yanzu,yana da muhimmanci a bawa tattaunawar kasashen duniya kann wannan batu damaJami’iyyar tsohon shugaban adawa na kosovo Hashim Thaci,itace ta lashe zaben ‚yan majalisar wakilai daya gudana ranar lahadi.Kazalika ministocin kasashen turan sun cimma matsaya guda dangane da faɗaɗa takunkumin su akan gwamnatin mulkin soji na Myanmar,adai dai lokacin da ake cigaba da kira ga taron kungiyar ƙasashen yankin kudu maso gabashin Asia da zai gudana a wannan mako a Singapore,daya dauki tsauraran matakan hukunci kann gwamnatin na Myanmar.