1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron ministocin harkokin wajen NATO

December 3, 2009

A yau ne ministocin harkokin wajen ƙungiyar tsaro ta NATO suka fara wata tattaunawa a birnin Brussels

https://p.dw.com/p/KpqL
Tutar ƙungiyar NATOHoto: DW/AP

Taron yazo kwana ɗaya bayan da Shugaban ƙasar Amirka Barack Obama ya bada sanarwar tura ƙarin sojoji dubu 30,000 izuwa ƙasar Afghanistan. Don haka taron zai maida hanakaline bisa samar da tsaroro a ƙasar ta Afghanistan.

A duk makon da ya gabata sakataren ƙungiyar tsaro ta NATO Anders Fogh Rasmussen, yana ta kai kawo tsakanin ƙasashen ƙungiyar don shawo kansu, bisa samar da ƙarin dakaru a ƙasar ta Afghanistan ƙarƙashin jagorancin ISAF. Don haka Rasmussen ya ce wannan batun samar da zaman lafiya a Afghanistan, bawai matsalace ta ƙasar Amirka kaɗai ba.

"Wannan ba yaƙin Amirka ce kaɗai ba, abinda ke faruwa a Afghanistan yana iya kawo hatsari ga dukkan al'ummar ƙasashen mu".

Komandan dakarun ƙawance a ƙarƙashin ƙungiyar ISAF, Janaral Stanley McChristal, ya buƙaci Amirka da ta kai ƙarin soji dubu 40. Bayan kai ruwa rana Shugaba Obama a ranar laraba ya sanar da yawan ƙarin dakrun da ƙasar za ta aika.

"Ya na daga cikin mahimmancin biyan buƙatar mu, na kai ƙarin soji dubu 30 izuwa Afghanistan"

Wannan yana nufin a ana buƙatar cika makon soji dubu 10, abinda Amirka take jiran ƙawayenta dake ƙungiyar NATO su cikata. Sakataren ƙungiya ta NATO Rasmussen ya ce a shekara mai zuwa za'a samu ƙarin dakaru dubu 5, ko kuma fiye da haka.

Anders Fogh Rasmussen Flash-Galerie
Sakatare janar na ƙungiyar NATO Anders Fogh RasmussenHoto: picture-alliance/ dpa

"Ƙasashen da bana Amirkawa ba dake cikin wannan ƙawance, za su aika da mafi ƙaranci na dakaru dubu biyar, za'a iya samun ƙarin wassu dubbai akai"

Izuwa yanzu wassu daga ƙasashen da ke da soji a Afghanistan, sun bada sanarwar aikawa da ƙari. Misali ƙasar Jojiya za ta tura dakaru 770, Turkiya za ta aika da ƙarin dakaru 800, Poland itama ta ce za ta aika da ƙarin dakru 600, yayin ƙasar Jamus taƙi cewa kamai har sai bayan taron Afghanistan da za'ayi cikin watan junairu a Birnin London. Ƙasar Jamus na mai cewa kafin wanan lokaci zasu ga irin sauyin da zai biyo bayan zaɓen Afghanistan. Iji ministan harkokin wajen Jamus Guido Westerwelle.

Westerwelle / Außenminister / Prag
Ministan harkokin wajen Jamus Guido WesterwelleHoto: AP

"Wata mahawar da akeyi a nan ƙasar mu ita ce, shin ƙarin yawan soji nawane za mu aika, ƙarin yawan soji nawa ya kamata mu aika, mu irin wannan mahawar ba mai karɓuwa bace a garemu"

To sai dai minstan harkokin wajen Jamus ɗin, yayi maraba da sanarwar shugaba Obama, wanda ya ƙiyasta cewa, za'a fara janye dakarun ƙawance a shekara ta 2011. Don haka Westerwelle ya ce sam matakin soji ba zai warware rikicin Afghanistan ba, illa dai kawai a ta farkin siyasa.