1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron ministocin harkokin wajen kasashen kungiyar EU game da halin da ake ciki a Darfur

Mohammad Nasiru AwalJuly 27, 2004
https://p.dw.com/p/Bvhk
´Yan gudun hijirar yankin Darfur a yammacin Sudan
´Yan gudun hijirar yankin Darfur a yammacin SudanHoto: AP

A wata ganawa da suka yi a karshen makon jiya ministan harkokin wajen Sudan Mustafa Osman Isma´il ya tabbatarwa shugaban majalisar shawara ta Turai wato ministan harkokin wajen kasar Netherlands, Bernard Bot, cewar gwamnatin Sudan na duk iya kokarin ta don ganin an kawo karshen ta´asar da sojojin sa kai larabawa ke yi a yankin Darfur. To sai dai gwamnatin birnin Khartoum na bukatar lokaci kafin ta iya yin haka. Hasali ma yanzu makonni uku kadai suka wuce daga cikin wa´adin kwanaki 90 da aka yarje da MDD don yin haka. Duk da haka dai Bernard Bot bai gamsu da ba, kamar yadda ya nunar bayan tattaunar da yayi da takwarorinsa 24 na kasashen KTT.
"Duk da alkawuran da aka dauka, har yanzu majalisar shawarar na nuna damuwa, domin ba´a samu wani ci-gaba ba. Muna kara samun rahonnin take hakkin dan Adam, wato ke nan har yanzu ba ta canza zane dangane da halin tsaro a Darfur, saboda haka ba zamu yarda da wannan hali da ake ciki."

Alkalumman da MDD ta bayar sun yi nuni da cewa mutane kimanin dubu 30 sun rasa rayukansu a wannan rikicin da ake yi da ´yan takifen Larabawan janjaweed a yankin na Darfur. Sannan kimanin miliyan daya sun tsere daga wannan yanki. Duk da haka ministocin harkokin wajen na kungiyar EU ba su fito fili sun yi barazanar kakabawa gwamnatin Sudan takunkumi ba, amma mista Bot ya ce har in ba´a samu kyautatuwar halin da ake ciki, to kungiyar EU zata fara tattauna batun sanyawa Sudan takunkumi a cikin watan satumba. Ministocin kuma ba su tattauna game da shawarar da Britaniya ta bayar na tura dakarun samar da zaman lafiya daga Turai ba. To amma an jiyo ministan harkokin wajen Jamus Joschka Fischer yana cewa.

"Ra´ayi ya zo daya cewar da akwai bukatar sanyawa gwamnatin Sudan takunkumi, har in ba ta cika alkawuran da ta dauka a cikin kankanen lokaci ba."

Fischer ya kara da cewa kwamitin sulhu na MDD kadai zai tsayar da wannan lokaci. To sai dai a birnin New York din ma ra´ayi ya bambamta a shawarwarin da aka yi cikin makon jiya, duk da kirar da sakatare-janar na MDD yayi na a gaggauta daukar matakan da suka dace bisa manufa.

A gun taron na jiya dai kungiyar EU ta yiwa kungiyar tarayyar Afirka tayin ba ta taimakon kudi don ta tura wata rundunar sa ido a Darfur, sannan a lokaci daya kuma kungiyar ta EU ta ware kudi EURO miliyan 200 a matsayin taimakon jin kai ga ´yan gudun hijirar yankin na Darfur.