Taron ministocin harkokin wajen EU akan iran a London | Labarai | DW | 06.10.2006
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron ministocin harkokin wajen EU akan iran a London

Ministocin harkokin waje na kasashe biyar masu zaunanniyaer kujera a komitin sulhun mdd,da suka hadar da Britania da Sin da Faransa da Rasha da Amurka,da kuma Jamus,sun gudanar da wani taro yau a birnin London,domin nazari kann yiwuwar daukan matakan ladabtar da Iran kann shirin Nuclearnta.Amurka,tare da goyon bayan Britania dai,zata tursasa bukatar kakabawa Iran takunkumi ,sai dai kasashen Sin da Rasha na adawa da hakan.Wannan taron na yau dai ya biyo bayan,yunkurin da jamiin kula da harkokin ketare na kungiyar KGT Javier Solana yayi nakarkato da Iran daga bunkasa sinadran Uranium dinta.Bayan kokarin nasa dai,Solana ya bayyana cewa babu wata madafa da aka cimma tsakanin bangarorin biyu,sai dai zaa cigaba kokari.Amurka da sauran kasashen yammaci na tsoron cewa,Iran na kera makaman Nuclear,ayayinda ita kuwa ta hakikance cewa,harkokin Nuclearnta na samarda makamashi ne.

 • Kwanan wata 06.10.2006
 • Mawallafi Zainab A Mohammad
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bu5C
 • Kwanan wata 06.10.2006
 • Mawallafi Zainab A Mohammad
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bu5C