Taron ministocin harakokin wajen G8 a Postdam | Labarai | DW | 30.05.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron ministocin harakokin wajen G8 a Postdam

Ministocin harakokin waje, na ƙasashen ƙungiyar G8, sun buɗa zaman taro a birnin Postdam, dake kussa da Berlin, a ci gaba da shirye-shiryen taron ƙoli da zai haɗa shugabanin wannan ƙasashe 8, mako mai zuwa a nan ƙasar Jamus.

Ministocin za su tsaida ruwan miya, a game da batutuwan da shugabanin za su tantana kan su, albarkacin taron.

Wasu daga wannan batutuwa, sun haɗa da rikicin yankin Darfur da kuma makaman nukleyar ƙasar Iran.

Sakatariyar harakokin wajen Amurika Condoleesa Rice, ta bukatacin takwarorin ta, su ƙara matsa ƙaimi ga hukumomin Teheran, a dangane da taurin kan da su ke nunawa, na ƙin yi watsi da aniyar mallakar makamin nuklea.

A nasa gefe, ministan harakokin wajen Jamus Frank Wlter Steinemeir, ya kira ga Amurika, ta bada haɗin kai ga yunƙurin dunia, na yaƙi da gurɓacewar yanayi.

Bisa dukkan alamu, akawai matuƙar wuya ƙasashen 8, su ka cimma daidaito,a kann batutuwan da aka jera a ajendar taron.