Taron ministocin harakokin wajen G8 a Mosco. | Labarai | DW | 29.06.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron ministocin harakokin wajen G8 a Mosco.

Yau ne sakatariyar harakokin wajen Amurika Condoleesa Rice, da takwarorin ta na ƙungiyar G 8,, su ka fara tantanawa a birnin Mosco na ƙasar Rasha.

Wannan haɗuwa, da ke matsayin share fage, ga taron ƙoli, da zai haɗa shugabanin ƙungiyar G8, a watan mai kamawa, z ata maida hankal,i a kan halin da a ke ciki, a ƙasar Irak, da kuma rikicin makaman nukleyar Iran.

Kazalika ministocin, za su tantana rikicin Afghanistan, inda a yau ma, soja ɗaya na rundunar kawance ya rasa ransa.

Jim kaɗan kamin ta baro Amurika, Condoleesa Rice, ta shaidawa manema labarai cewa za su yi anfani da wannan dama, domin ƙara kira, ga gwamnatin Hamas na Palestninu, da ta bada kai, bori ya hau, a kira da ƙasashen dunia ke mata, na kwance ɗamara, da kuma amincewa da Isra´ila, a matsayin ƙasa mai cikkaken yanci.

Saidai, a ɗaya hannun, Rice ta ce Amurika na bada goya baya, ga harin da Isra´ila ta kai a zirin Gaza, domin ƙwato sojan ta, da a kayi garkuwa da shi.