1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron ministocin harakokin wajen ƙasashen larabawa a Khartum

Ministocin harakokin waje, na ƙasashen larabawa, sun fara zaman taron share fage, a birinin Khartoum na ƙasar Sudan, a shirye shiryen taron ƙoli, na shugabanin ƙasashe da za ayi, a Sudan, daga 28 zuwa 29 ,ga watan da mu ke ciki.

Baki ɗaya ƙasashe 22, na yankin larabawa sun tura tawagogin su a wannan taron na yini 2.

Mahimman batutuwan da su ke tantananawa akai, sun haɗa da rikicin ƙasar Iraki, da kuma halin da ake ciki, tsakanin, Israela da Palestinu, da irin rawar da ya cencenta ƙasashen larabawa su taka, domin kawo ƙarshen rigingimu, da ke ci gaba da tada zaune tsaye, a yankin gabas ta tsakiya.

Ta wannan fanni,ministocin sun yanke shawara, sake gabatar da daftarin zamna lahia, da shugabanin ƙasashen larabawa, su ka cimma daidaito akai, a taron birnin Beruth a shekara ta 2002.

Ministan harakokin wajen Iraki, da ke halartar wannan taro, ya bukaci ƙasashen larabawa su bada tallafi, domin samar da zamna lahia Iraki, sannan su yafe bassusukan da su ka tambayo ƙasar.

Saidai a yayin da ya rage kwanaki 3 rak, a fara taro ƙolin maijiyoyi masu ƙarfi, na nuni da cewa,wannan ba zai tsinana wani abun a zo a gani ba.

Tunni wasu daga shuhabanin, sun bayyana cewa ba za su hallartar taron ba.

A nasu ɓangare hukumomin Khartoum, na zargin Amurika da kitsa maƙarƙashiya, don kar taron ya cimma nasara.