1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron ministocin harakokin waje na kasashe membobin kungiyar gamayya turai.

Nan gaba a yau ne ministocin harakokin waje na kungiyar gamaya turai, ke fara zaman taro, inda za su tantana batutuwa daban daban, da su ka hada da na kudaden assusun kungiyar na shekara ta 2007 zuwa 2013.

A wani zaman taro makamacin wannan ,da ministocin su ka shirya, a watan yuni da ya wuce, sun watse baran- baran, ba tare da cimma nasara tsaida pasalin wannan assusu ba, a dalili da kiki kakar da a ka fuskanta.

Kasar Fransa ta yi tsayuwar gwamen jaki, a game da bukatar Britania, na rage yawan kudaden da kungiyar EU ke sakawa ta fannin noma.

A nata gefe, Britania, ta hau kujera naki, ga bukatocin sauran kasashen kungiyar Gamaya turai, na rage yawan moriyar kudaden assusun Eu da ta ke ci.

Bayan batun assusun ministocin za su tantana a kan harakokin cinikaya, a jajibirin taron da kungiyar zata yi, da kasashen Japan, Brazil, India, da Amurika a game da harakokin kasuwa.