1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron ministocin harakokin kuɗi na Afrika a Ouagadougou

Yahouza SadissouMay 15, 2006

Ministocin harakokin kuɗi na nahiyar Afrika, da ƙurrarun massana ta fannin tattalin arziki sun gudanar da taron yini 2 a birnin Ouagadougou na Burkina Faso

https://p.dw.com/p/Bu05

Ministocin kuɗi na ƙasashen Afrika, da wasu ƙurraru ta fannin tattalin arziki, sun gudanar da taron yini 2, a birnin Ouagadougou na ƙasar Burkina Faso.

Mahalarta wannan taro, sun hito daga sassa daban-daban na Afrika, domin tantanawa akan batutuwan da su ka jiɓanci harakokin tattalin arziki a nahiyar, da kuma mattakan bunƙassa kampanoni da masana´antu, ƙanana da manya,da zumar samar da ayyukan yi, ga matasa, wanda a halin yanzu ke fama da matsalolin zaman kashe wando.

Ƙurrarun masana ta fannin tattalin arziki, da su ka halaraci wannan taro, sun nunar da cewa, an samu ɗan ci gaba, a nahiyar Afrika daga shekara ta 2000 zuwa bana, to saidai wannan ci gaba, bai taka kara ya karya ba, domin bai isa, ya kawo ƙarshen matsalolin talauci da fatara, da al´ummomin nahiyar ke fama da su.

Wannan taro, ya biwo bayan taron ƙolin shugabanin ƙasashen Afrika, da ya gudana, yau da shekaru 2, a birnin Ouagadougou.

A ƙarshen taron na shekara ta 2003, shugabanin ƙasashen Afrika, su ka alkawarta ,tuntubar juna, domin bitar halin da ake ciki, ta fannin samar da guraben aiki ga matasa ta fannin yaƙi da cin hanci da rashawa, da kuma bunƙasa harakokin noma, da cuɗe ni in cuɗe ka, tsakanin ƙasashen nahiyar.

Shugaban banki raya ƙasashen Afrika Donald Kaberuka, ya tabatar da cewa, haƙiƙa!!! an samu ci gaba,mussamman ta hanyar girka kampanoni da masana´antu masu zaman kansu, to amma idan a ka kawatata, da yanayin sauran ƙasashen dunia, Afrika na da sauran rina kaba.

Ministar harakokin kuɗi ta tarayya Nigeria, Ngozi Okonjo-Iweala, da ke halartar taron,ta ce duk da yake, an samu ci gaba a tsawan shekaru 2 da su ka wuce, bai kai mizanin ma´aunin da Majalisar Dinkin Dunia ta ƙayyade ba,na rage talauci a Afrika, nan da shekaru 10 masu zuwa.

Ministar ta jaddada mahimamancin bada ƙarfi ga harakokin noma, wanda su ne tushe arziki, da kuma samar da ayyukan yi a nahiyar Afrika.

Saidai wasu daga mahalarta sun nuna aadwa da fido wata sabuwar sanarwa a game yaki da zaman kashe wando.

Alal misali ministan harakokinkudi na kasar Botswana Duncan Mlazie ya bayyana kamapanin dullancin Reuters cewar bai ga anfanai sake hido da wata sanarwar ta la´akari da a yanzu haka akwai sanaryoyi da dama da aka hido wanda kuma bqa su anfana komai ba, ta fannin yaki da talauci a nahiyar Afrika.

Shikuma ministan kuɗi na Afrika ta kudu, Trevor Manuel, ya gabatar da lacca, inda ya soki ƙasashen Afrika masu albarkatun man petur, da yin watsi kwata kwtaa da harakokin noma.

Sannan, ya ja hankullan mahalarta taron, a game da matsalar kwararar Afrikawa, zuwa ƙasashen ƙetare, da zumar samun aikin yi, a yayin da al´ummomin wasu nahiyoyin ke shigowa Afrika, don samun ayyuka.