Taron ministocin harakokin cigin gidan kasashen EU | Labarai | DW | 20.04.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron ministocin harakokin cigin gidan kasashen EU

Ministocin cikin gida na EU sun shiga zaman taro yau juma’a akan samun bakin zaren warware matsalolin ‘yan gudun hijiran Iraqi. Kungiyoyin agaji suna kara matsin lamba ga kungiyar ta EU akan ta kara yawan ‘yan gudun hijiran da take dauka karkashin kulawan ta, wanda suke ganin zai taimaka wajen rage wahalolin da kasashe kamar su Jordan da Syria dake makwabtaka da Iraqi ke fama da su na ‘yan gudun hijira. Kasar Sweden tace zata yi anfani da wannan dama wajen janyo hankalin duniya kan halin da ‘yan gudun hijiran Iraqi ke ciki. Akalla ‘yan gudun hijira 20,000 daga Iraqi, suka shigar da takardun neman mafaka a kasashen EU a shekarar 2006.