Taron ministocin ciniki na EU da Arewacin Afrika da gabas ta tsakiya | Labarai | DW | 23.03.2006
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron ministocin ciniki na EU da Arewacin Afrika da gabas ta tsakiya

Ministocin ciniki na kungiyar gamayyar Turai EU,zasu gudanar da wata ganawa da takwarorinsu na kasashe arewacin Afrika da yankin gabas ta tsakiya a gone jummaa ,acigaba da kokarinsu na cimma muradin sakarwa harkokin kasuwanci a yankin tekun Mediterian nan da shekarata 2010.Ministocin wadanda zasu gudanar da wannan taro nasu a birnin Marrakech dake kasar Moroko ,zasu tattaunawa yadda yan kasuwa zasu samu sukunin tafiyar da harkokinsu a yankin mediterian ,wanda ya jima ana kokarin cimma a shekaru 10 da suka gabnata.Ministan ciniki na EU Peter Mandelson yace,yin hakan zai taimakawa yan kasu daga bangarorin biyu tafiyar da harkokin kasuwancin su cikin sauki.

 • Kwanan wata 23.03.2006
 • Mawallafi Zainab A Mohammad
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bu7K
 • Kwanan wata 23.03.2006
 • Mawallafi Zainab A Mohammad
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bu7K