Taron ministocin cikin gidan EU | Siyasa | DW | 16.01.2007
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Taron ministocin cikin gidan EU

Ministocin cikin gidan ƙasashen Eu sun kammala zaman taro a game da baƙin haure

default

Ministocin harakokin cikin gida na ƙasashe membobin ƙungiyar gamayya turai, sun kammala zaman taro, a birnin Dresde dake gabancin ƙasar Jamus.

Taron na birnin Dresde, da ya haɗa illahirin ministocin cikin gida na ƙasashen EU, ya maida akala kacokam, a game da matsalolin baƙin haure da ke ciwa ƙasashe turai tuwo a ƙwarya.

Bayan masanyar ra´yoyi ta yini ɗaya, ministocin sun gano cewar ya zuwa yanzu, babu nasara da a ka cimma ta killace kwarar baƙin haure zuwa turai, duk kuwa da matakkan haɗin gwiwa da ƙasashen su ka tanada.

A sakamakon haka, komishinan EU, mai kulla da harakokin baƙi, Franko Frattini, ya bayyana wasu sabin shawarwari wanda ƙila, za su taimaka, a magance wannan matsala.

Wannan shawarwari, sun haɗa da baiwa Frontex,issasun kayan aiki, wato hukumar haɗin gwiwa, dake sintiri a iyakokin tekun Turai da Afrika, domin laluƙo baƙin haure masu niyar shiga turai ta ɓarauniyar hanya.

A wata shawara kuma, Franko Frattini, ya bukaci ƙasashen turai, su ɓullo da wani saban tsari, na gudanar da kwaskwarima ga yaƙi da baƙin haure.

Ya shawarci ministocin ƙwadago, na EU da su keɓe guraben aiki, ga baƙin haure, wanda maimakon su shiga ta ɓarauniyar hanya , za su samu Visa mai basu damar aiki na ƙayaddaden lokaci, wanda kuma zai basu damar samun jalli idan sun koma ƙasashen su na assuli.

Saidai wannan mataki, ba zai cimma nasara ba,sai in baƙin sun amince su koma gida, da zaran kwantarangin aikin su ya kai ƙarshe.

Shima ministan cikin gidan Jamus, ya yi lale marhabin da wannan shawarwari, amma tare da haɗi karfi da ƙasashen Afrika da abun ya shafa.

Ƙasashe kamar su Mali, Senegal, gambia, da Mauritania na daga sahun wanda turai ke bukatar haɗin kai, daga gare su, domin cimma nasara a wannan saban tsari na magance matsalolin baƙin haure.

 • Kwanan wata 16.01.2007
 • Mawallafi Yahouza S. Madobi
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Btwc
 • Kwanan wata 16.01.2007
 • Mawallafi Yahouza S. Madobi
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Btwc