TARON MINISTOCIN AFRIKA DON YAKAR FARIN DANGO. | Siyasa | DW | 27.07.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

TARON MINISTOCIN AFRIKA DON YAKAR FARIN DANGO.

Ministocin kasashen nahiyar afrika,a yau talata suka gudanar da taro na musamman a babban birnin kasar Algeria wato algiers,inda suka tattauna irin matakan da ya kamata a dauka don yakar farin dango,da suka fara addabar kasashen arewaci da kuma yammacin nahiyar ta afrika,ta hanyar illata amfanin gona.

Hukumar kula da tallafin abinci ta majalisar dinkin duniya,a wajen wannan taro,ta kafa gidauniya inda ta nemi kasashen duniya da su bada tallafin su don samar da kudi har kimanin dalar amurka million tamanin da uku,wanda zaa yaki wannan annoba ta farin dango,wadanda ke lalata amfanin gonaki,a wasu sassan na nahiyar afrikan.

Shugaban wannan hukuma mai suna Joseph Tchikaya,cewa yayi a wajen taron,hukumar ta kaddamar da wannan gidauniya ne don samun hanya mafi sauki da kuma gaggawa ta yakar wannan annoba.

A binciken da hukumar ta gudanar,wanda ta bayyana sakamakonsa a yau din a wajen taron,ta tabbatar da cewa,kadan daga cikin wadannan fari,na iya cinye yawan hatsin da giwaye goma ko rakuma ashirin da biyar ko kuma mutane dubu biyu da dari biyar zasu ci a lokaci guda.

Ministoci daga kasashen dake fama da wannan annoba,wanda suka hada da na kasar Algeria da Chad da Libya da Mali da Mauritania da Morocco,da Niger da Senegal da kuma Tunisia,sun gudanar da wannan taro ne kamar yadda suka bayyana,don tattaunawa kann irin matakan da kowacce kasa ke dauka wajen magance wannan annoba.

Wanda bayan nan ne kuma zasu gudanar da wani taron nan gaba na hada karfin kasashen waje guda don yakar annoba da kuma tattauna matakan kare faruwar hakan anan gaba.

Mr Tchikaya,shugaban hukumar bada tallafin abinci ta majalisar dinkin duniya,cigaba yayi da cewa a wajen taron,har yanzu babu wani tabbaci akan alkawurran tallafi da hukumar ta fara samu,sai dai fatan samun tabbatuwarsu.

A tun farkon watannan ne da muke ciki,hukumar ta bayyana cewa wadannan farin dango sun shiga gonaki a kasashen Mauritania da Mali da Senegal.wanda kuma bincike ya tabbatar da cewa yawan farin zai karu a kasashen nan gaba.

A makwanni biyu da suka gabata kuwa rahotanni sun tabbatar da cewa yawan farin na ta karuwa a wadannan kasashe har ma suna dada fantsama izuwa wasu kasashen.

A kasashen yammacin nahiyar ta afrika an samu damina mai albarka,domin kuwa anyi shuka sosai a kasashe da dama,sai dai kuma wadannan fari duk sun lalata wannan amfanin gona bisa yadda rahotanni suka bayyana.

A kasashen Morocco da Libya,an gwada wani magani a kann farin wanda kuma ya taimaka kwarai wajen kashe wadannan kwari.Bisa hakan ne kuma,ake sa ran nan bada dadewa ba zaa samu galabar farin a wadannan kasashe.

A jawabinsa na rufe taron ne,prime ministan kasar Algeria,Ahmed Ouyahia,yayi kira ga mahalarta taron dasu yi kokarin hada kawunan su wajen tabbatuwar matakan da suka tattauna a taron,yin hakan a cewarsa shi zai bawa sauran kasashen da suke neman taimako wurinsu,karfin gwiwar bada tallafin.

Maryam L.Dalhatu.