1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron ministocin Afrika da na Turai a game da batun baƙin haure

Yahouza S. MadobiJuly 11, 2006

A birnin Rabat na ƙasar Marroko a na ci gaba da taron ministocin Afrika da na Turai a game da yaƙi da baƙin haure

https://p.dw.com/p/BtzH
Hoto: maec

Batun baƙin haure, ya zama ƙayar wuya, ga wasu ƙasashen turai da Afrika.

A tsawan kwanaki 2, ministocin na tantanana hanyoyin magance wannan matsala, da ke shirin zama gagarabadau.

A karo na farko, Afrika da turai, za su ɓullo da mattakan haɗin gwiwa, na yaƙi da yan gudun hijira, da ke kwarara daga Afrika zuwa ƙasashen turai, ta ɓarauniyar hanya.

A ranar jiya litinin, France da Spain ,sun gabatar da shawawari , wanda a tunanin su, ke iya kawo ƙarshen matsalar.

Ministan cikin gidan France, Nikolas Sarkozy, da a bayan bayan nan, ya hido da dokar yaƙi da baƙin haure, ya ce babban mataki, na ɓullowa matsalar shine, haɗa ƙarfi tsakanin ƙasashen asuli, da na yada zango, da kuma masu karɓar baƙin.

Nan gaba a yau, a ke sa ran, mahalarta taron su hiddo da sanarwar ƙarshe, wada zata shinfiɗa dokokin ƙayyade mattakan magance matsalar baƙin haure.

A nasa ɓangare,ministan harakokin wajen ƙasar Maroko, ya shawarci tanadar da matakai inganttatau, na yaƙi da talauci,da jahilci, da kuma zaman kashe wando, a ƙasashen Afrika, wanda su ne ummal ibasar da ke cilastawa matasan nahiyar Afrika, zuwa turai.

Shima ministan harakokin wajen Senegal, Cheick Tidjani Gadio, ya nunar da cewa, ya zama wajibi, ƙasashen turai su taimaka da kuɗaɗe masu yawa, domin girka masana´antu a Afrika, muddun su na buƙatar samun sassauci, ga kwararar Afrikawa a nahiyar turai.

A yayin da ya gabatar da jawabin sa, shugaban hukumar abinci ta Majalisar Ɗinkin Dunia, Jacques Diouf, yayi kira ga shugabanin ƙasashen Afrika, da su maida himma, wajen ayyukan noma, wanda su ne tushen arziki.

Ya buƙaci ganin, an tanadi hanyoyin ƙarfafa noman rani, musamman a yankunan Sahara da na Sahel, da ke fama da matsalolin ƙaracin ruwan sama.

A yayin da a ke gudanar da taron, hukumar zartaswa, ta ƙungiyar gamaya turai, ta bayana bada gudummuwa ta dalla milion 2, da rabi ga ƙasar Mauritania, domin yaƙi da baƙin haure, da ke kwarara zuwa tsibirin Canaries domin shiga turai.

Mamma Fanta, wata yar ƙasar Senegal, ta koka a kan yada su ke saida kadarorin su, domin taimakawa yara, zuwa ƙasashen turai nema abun dunia, amma a wayi gari haƙa ta kasa cimma ruwa.

To s